TheCable Fact Check
  • Home
  • Fact Check
  • Fake News
  • Check Am For Wazobia
Reading: Sabon shugaban Senagal ya kushe Faransa a bidiyon da ke yawo?
Share
Latest News
No, Emefiele no return N4trn to FG
Rárá, Emefiele kò dá triliọnu mẹrin náírà padà fún ijọba àpapọ̀ orílẹ̀ èdè Nàìjíríà
Ḿbà, Emefiele ènyéghàchìghị̀ FG ọ́nụ́ égó N4trn
A’a, Emefiele bai mayarwa FG N4trn ba
FACT CHECK: No, Emefiele didn’t return N4trn to FG
FAKE NEWS ALERT: Akume hasn’t been replaced as SGF, says presidency
Rárá, Nàìjíríà kò fi àwọn ọmọ iṣẹ́ ológun rán sẹ sí Ísírẹ́lì láti dá rògbòdìyàn tó ń ṣẹlẹ̀ níbẹ̀ dúró
Slurs, smears, slander… how gendered disinformation targets high-profile Nigerian women
Advertisement
Aa
TheCable Fact CheckTheCable Fact Check
Search
  • Home
  • Fact Check
  • Fake News
  • Check Am For Wazobia
Follow US

Sabon shugaban Senagal ya kushe Faransa a bidiyon da ke yawo?

Ahmad Sahabi
By Ahmad Sahabi Published April 5, 2024 4 Min Read
Share

Idan an yi amfani da shafukan sada zumunta kwanan nan, ba mamaki an ga wani bidiyo da ke nuna Bassirou Diomaye Faye, sabon shugaban kasar Senegal, ya na kushe Faransa.

Bidiyon – wanda ya na ta yawo a shafukan sada zumunta a Najeriya da wasu kasashen Afurka – na yawo a TikTok, X ( wanda a da aka sani da Twitter), Facebook, Linkedin, da kuma Whatsapp.

“Lokaci yayi da Farasa zata daina cin zali. Shekaru da yawa na mulkin mallaka, safaran mutane sun jefa mu cikin wahala. Lokaci yayi da zamu magance wannan abu,” inji mai magana a bidoyon.

Mutanen da ke tura bidiyon na yin hakan ne saboda murnar Faye zai zama shugaban kasa a Afurka mai mafi karancin shekaru, kuma yana sukar Faransa.

@von_Bismack mai mabiya sama da 100,000 a shafin sa na ya daura bidiyon a shafin sa a ranar Talata da rana.

Mutane sama da 20,000 sun gani, 32 sunyi sharhi a kai, 500 sun danna alaman so, sannan 333 sun sake turashi. A danna nan domin ganin bidiyon.

“Lokaci yayi da Faransa zata kyale Afurka”…. inji mista Bassirou Diomaye Faye, sabon shugaban Senegal. Hakan na nuna bakin jinin da Faransa keda Afurka,” inji rubutun da aka yi a karkashin bidiyon.

A Facebook O’Kay Adedayo ya saka bidiyon a shafin sa tare da rubutun: “Afurka ta farka. Allah ya kare sabom shugaban Senegal. Saura Najeriya a 2027.

A Whatsapp ma mutane na da tura bidiyon.

TABBATARWA

TheCable ta yi bincike a kan bidiyon inda ta gano cewa bidiyon an yanko shi ne daga wani jawabi da Ousmane Sonko, tsohon shugaban ‘yan adawa a Dakar, Senegal a 2021.

Sonko kuma da yake jawabin sa a yaren Faransanci yayi ba da turanci ba.

Ya zargi kasashen turai da cewa sune suka hana wuraren da suka mulka samun ci gaba.

A gaba daya jawabin sa da aka haska a Youtube a shafin Senegal 7, mai tsawon awa daya da minti talatin, Sonko da faransanci yayi magana.

Ya kuma daura rubutun jawabin nasa a shafin sa na Twitter shima duk a Faransancin.

Mun gano cewa bidiyon da ake cewa sabon shugaban Senegal ne yayi yana kan Youtube tun 2023.

SONKO DA FAYE NA DA ALAKA?

Sonko shine shugaban jami’iyar Patriots of Senegal (PASTEF), jam’iyar da Faye ya lashe zabe da.

Kwararru a fannin siyasa na cewa Faye yaron Sonko ne na siyasa. Dukkan su kafun yin zabe a tsare su kafun a ka sake su daga baya.

Kotun kolin kasar ta dakatar da Sanko daga yin takarar shugaban kasa, wanda hakan PASTEF ta tsaida Faye a matsayin da takarar ta.

HUKUNCI

Mai magana a bidiyon wanda ke sukar Faransa ba Faye, sabon shugaban Senegal bane. Sonko ne, shugaban jam’iyar PASTEF. Bidiyon da ke yawo an yanke wani bangare ne na wani jawabin da Sonko yayi a 2021.

TAGGED: Bassirou Faye, France, Senegal

Please send your feedback, claims to fact check and corrections requests to [email protected]

Ahmad Sahabi April 8, 2024 April 5, 2024
Share this Article
Facebook Twitter Email Copy Link Print
Leave a comment Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

POPULAR POSTS

Advertisement

No, Emefiele no return N4trn to FG

One video wey dey waka for social media show as Facebook user claim sey Godwin…

July 4, 2025

Rárá, Emefiele kò dá triliọnu mẹrin náírà padà fún ijọba àpapọ̀ orílẹ̀ èdè Nàìjíríà

Fídíò kan tí àwọn ènìyàn ti ń pín lórí àwọn ohun ìgbàlódé íbaraẹnise orí ayélujára,…

July 4, 2025

Ḿbà, Emefiele ènyéghàchìghị̀ FG ọ́nụ́ égó N4trn

Ótù ihe ngosị nà soshal midia egosila ebe ótù onye ji Facebook ekesa ozi kwuru…

July 4, 2025

A’a, Emefiele bai mayarwa FG N4trn ba

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani ma’abocin Facebook…

July 4, 2025
Advertisement
Advertisement

YOU MAY ALSO LIKE

No, Emefiele no return N4trn to FG

One video wey dey waka for social media show as Facebook user claim sey Godwin Emefiele, di forma govnor of…

CHECK AM FOR WAZOBIA
July 4, 2025

Rárá, Emefiele kò dá triliọnu mẹrin náírà padà fún ijọba àpapọ̀ orílẹ̀ èdè Nàìjíríà

Fídíò kan tí àwọn ènìyàn ti ń pín lórí àwọn ohun ìgbàlódé íbaraẹnise orí ayélujára, tí ó ṣe àfihàn ẹni…

CHECK AM FOR WAZOBIA
July 4, 2025

Ḿbà, Emefiele ènyéghàchìghị̀ FG ọ́nụ́ égó N4trn

Ótù ihe ngosị nà soshal midia egosila ebe ótù onye ji Facebook ekesa ozi kwuru na Godwin Emefiele, onye bụbu…

CHECK AM FOR WAZOBIA
July 4, 2025

A’a, Emefiele bai mayarwa FG N4trn ba

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani ma’abocin Facebook yana ikirarin Godwin Emefiele, tsohon…

CHECK AM FOR WAZOBIA
July 4, 2025

CableCheck seeks to provide reliable tools and resources for readers to tackle the menace of fake and misleading materials constantly pushed into the public space from various sources. We monitor the accuracy of claims made in traditional and social media. We also provide a tracker to hold politicians and policymakers accountable for the plans and promises they make to the public. CableCheck is a project of the Cable Newspaper Journalism Foundation (CNJF), supported by the MacArthur Foundation and implemented by TheCable newspaper.

Follow US: 

LINKS

  • Contact
  • About Us
  • Non-Partisanship Policy
  • Funding
  • Correction Policy
© Copyright TheCable. All Rights reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?