Idan an yi amfani da shafukan sada zumunta kwanan nan, ba mamaki an ga wani bidiyo da ke nuna Bassirou Diomaye Faye, sabon shugaban kasar Senegal, ya na kushe Faransa.
Bidiyon – wanda ya na ta yawo a shafukan sada zumunta a Najeriya da wasu kasashen Afurka – na yawo a TikTok, X ( wanda a da aka sani da Twitter), Facebook, Linkedin, da kuma Whatsapp.
“Lokaci yayi da Farasa zata daina cin zali. Shekaru da yawa na mulkin mallaka, safaran mutane sun jefa mu cikin wahala. Lokaci yayi da zamu magance wannan abu,” inji mai magana a bidoyon.
Mutanen da ke tura bidiyon na yin hakan ne saboda murnar Faye zai zama shugaban kasa a Afurka mai mafi karancin shekaru, kuma yana sukar Faransa.
@von_Bismack mai mabiya sama da 100,000 a shafin sa na ya daura bidiyon a shafin sa a ranar Talata da rana.
Mutane sama da 20,000 sun gani, 32 sunyi sharhi a kai, 500 sun danna alaman so, sannan 333 sun sake turashi. A danna nan domin ganin bidiyon.
“Lokaci yayi da Faransa zata kyale Afurka”…. inji mista Bassirou Diomaye Faye, sabon shugaban Senegal. Hakan na nuna bakin jinin da Faransa keda Afurka,” inji rubutun da aka yi a karkashin bidiyon.
A Facebook O’Kay Adedayo ya saka bidiyon a shafin sa tare da rubutun: “Afurka ta farka. Allah ya kare sabom shugaban Senegal. Saura Najeriya a 2027.
A Whatsapp ma mutane na da tura bidiyon.
TABBATARWA
TheCable ta yi bincike a kan bidiyon inda ta gano cewa bidiyon an yanko shi ne daga wani jawabi da Ousmane Sonko, tsohon shugaban ‘yan adawa a Dakar, Senegal a 2021.
Sonko kuma da yake jawabin sa a yaren Faransanci yayi ba da turanci ba.
Ya zargi kasashen turai da cewa sune suka hana wuraren da suka mulka samun ci gaba.
A gaba daya jawabin sa da aka haska a Youtube a shafin Senegal 7, mai tsawon awa daya da minti talatin, Sonko da faransanci yayi magana.
Ya kuma daura rubutun jawabin nasa a shafin sa na Twitter shima duk a Faransancin.
Mun gano cewa bidiyon da ake cewa sabon shugaban Senegal ne yayi yana kan Youtube tun 2023.
SONKO DA FAYE NA DA ALAKA?
Sonko shine shugaban jami’iyar Patriots of Senegal (PASTEF), jam’iyar da Faye ya lashe zabe da.
Kwararru a fannin siyasa na cewa Faye yaron Sonko ne na siyasa. Dukkan su kafun yin zabe a tsare su kafun a ka sake su daga baya.
Kotun kolin kasar ta dakatar da Sanko daga yin takarar shugaban kasa, wanda hakan PASTEF ta tsaida Faye a matsayin da takarar ta.
HUKUNCI
Mai magana a bidiyon wanda ke sukar Faransa ba Faye, sabon shugaban Senegal bane. Sonko ne, shugaban jam’iyar PASTEF. Bidiyon da ke yawo an yanke wani bangare ne na wani jawabin da Sonko yayi a 2021.