A ranar 14 ga watan Yuni, wani shafin Twitter mai dauke da sunan Olusegun Obasanjo ya bayyana Peter Obi a matsayin mutum mai gaskia da amana.
Shafin twittern, lokaci zuwa lokaci yana tura labarai akan tsohon shugaban kasa. Shafin nada mabiya kusan mutane dubu biyar (5,000) a lokacin da aka tura maganan da Obasanjo yayi akan Obi, kuma a yanzu mabiyan shafin ya karu zuwa mutane dubu goma (10,000).
“Shi ba Waliyyi bane, amma a cikin yan siyasan Nijeriya a yau, Peter Obi mutun ne mai gaskia da amana,” rubutun da akayi kenan tare da daura.
Mutane sama da dubu talatin da uku (33,000) sun danna alaman so wa labarin, kuma mutane sama da dubu takwas (8,000) sun tura labarin sannan mutane dari tara (900) sunyi sharhi akan labarin.
Wasu masu shafi a twitter da suka ga labarin sun nuna jin dadin su ga yabon da Obasanjo yayi ma Obi.
Festus Agene, yayi sharhi akan labarin inda yace ” Yabo me kyau daga Baba OBJ”.
A good validation from Baba OBJ…I am OBIdient https://t.co/fHyFboX4GG
— Primus1 (@firsty1_) June 16, 2022
https://twitter.com/DaveZaint/status/1537346351062732800?s=20&t=mGW5AhqUbnWzSpAXHYqQ1w
He is not a saint but among politicians in Nigeria today, Peter Obi is a bundle of integrity. pic.twitter.com/M3THSJWqS2
— Olusegun Aremu Obasanjo (@Oolusegun_obj) June 15, 2022
David Gas, a cikin sharhin nasa, ya ce, “Gaskia da Amana suna da wuyar samu a cikin ‘yan siyasarmu a yau, amma Peter Obi mutum ne mai wadannan halaye. Na gode kuma na gode wa Olusegun Obasanjo saboda ra’ayinsa na gaskiya”.
TABBATARWA
Wani binciken a yanar gizo ya nuna cewa, babu wani kafar yada labarai daya buga maganan da tsohon shugaban kasa yayi.
Da TheCable ya tuntubi Kehinde Akinyemi, mai magana da yawun Obasanjo, yayi watsi da maganan, inda yace tsohon shugaban kasa beyi wannan maganan akan Obi ba.
Ya ce Obasanjo bai yi irin wannan magana a Twitter ko a shafukan sada zumunta ba.)
HUKUNCI
Labarin dake yawo a kafafen sada zumunta dake cewa Obasanjo ya mara wa Peter Obi baya ba gaskiya bane.
Labarin ya fito ne daga shafin karya na Twitter wanda ba na Olusegun Obasanjo ba.