Wani rubutu da aka wallafa a dandalin sada zumunta ya yi ikirarin cewa istimna’i na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da asarar gashi ga maza.
Rubutun wani mai shafi a Twitter, Eric @amerix ya fara shi, inda yace yawan yin inzali zai iya janyo gashi ya daina fitowa a kan maza.
“Daya daga cikin abubuwan farko na asarar gashi shine istimna’i. Yawan yin inzali na sa a rasa kayan gina gashi a cikin jiki. Duk sanda aka gamu da mutumin da gashin kansa ya daina fitowa, a tuna mishi da maganan nan,” inji rubutun.
One of the primary causes of hair loss is MASTURBATION.
Indiscriminate ejaculation leads to the intentional loss of vital nutrients responsible for hair growth.
Every time you meet a man with a receding hairline, remind him about semen retention.#BetterTogether
— Eric (@amerix) August 23, 2022
Gidan ya tattara sama da 1, 400 retweets da 8, 800 likes.
A Facebook, an raba wannan sakon sau da yawa akan asusu daban-daban. Daya daga cikin irin wadannan shine Emem Nelson wanda ke ikirarin shi likita ne mai mabiya sama da 8,000.
Wani mai amfani, Jay Ade ya sake buga da’awar akan Medriod Elite City, ƙungiyar jama’a akan Facebook wanda ke da mabiya sama da 9,000.
Tabbatarwa
Kamus na Merriam-Webster ya ayyana istimna’i a matsayin motsa jiki, musamman na gabobin al’aurar mutum wanda ke haifar da inzali.
Bisa ga ma’anar, ana iya samun istimna’i ta hanyar hannu ko wasu hulɗar jiki ba tare da jima’i ba, ta hanyar amfani da kayan aiki, lokaci-lokaci ta hanyar tunanin jima’i, ko ta hanyar haɗuwa daban-daban na waɗannan hukumomin.
TheCable ta tuntubi kwararrun likitoci don tabbatar da ko akwai wata hujja ta kimiyya da za ta tabbatar da da’awar cewa al’aura ko fitar da maniyyi ba gaira ba dalili na iya haifar da asarar gashi.
Best Ordinioha, wani farfesa a bangaren kiwon lafiya, yayi watsi da maganan, yace babu abun da ya hada tsinkewan gashi da wasa da gaba don biyan bukata.
A cewarsa, mai yiwuwa mai amfani da Twitter ya fitar da irin wannan sakon ne don jawo hankalin jama’a zuwa shafinsa
“Ina tunanin kawai yayi hakan ne domin ya yada maganan, wanda yin hakan kuma zai iya janyo wa mazan da gashin su ya daina girma idan aka gansu, za a fara tunanin abun da sukeyi kenan gashin su ya daina girma,” inji farfesa a bangaren kiwon lafiya.
“A bangaren kiwon lafiya, karuwan testosterone ne ke janyo gashi ya daina fitowa. Har ila yau, a bangaren kimiyya, babu wani shaida da ya goyi bayan maganan cewa yawan yin inzali na janyo rashin gashi ba.
“Wadanda suka fi yawan testosterone a jikin su zasu iya fin karfin sha’awa amma wannan abun zai iya raguwa da abubuwa da yawa: kasala zai iya sa mutum ya kasa haihuwa, kuma jima’i ne kila abu na karshe dake cikin zuciyarsu. Ina tunanin wanda ya tura maganan ya zuzuta shi.”
Labari da ake Yiwa rashin gashi
Francis Agbaraolorunpo, kwararre a fannin kiwon lafiya a jami’ar Legas, ya ce abubuwa biyu da suka hada da kwayoyin halitta, yanayin kiwon lafiya da yawan amfani da sinadarai na iya haifar da zubar gashi ga maza, amma ba shakka ba istimna’i ba ne.
“Daya daga cikin mahimman abubuwan da ke haifar da asarar gashi shine kwayoyin halitta, an haifi mutum da hali. Wani abu kuma shi ne mutum na iya gadon sa daga iyaye,” inji shi.
“Wasu mutanen da ke da alopecia ko yanayin rashin lafiya kamar su kansa ma na iya rasa gashin kansu. A wannan yanayin, mace kuma za ta iya samun asarar gashi.
“Idan ka ga mutum da gashin kansa ya ja baya, mai yiyuwa ne akwai kwayar halitta a cikin iyali, yana iya zama kwayar halittar da ba a bayyana ba, amma ana iya bayyana shi lokacin da kwayar halitta ta dace da wasu yanayi.”
Sai dai kwararen likitan ya jaddada cewa ciwon gabobi ya fi zama matsala ta tunani kuma ba shi da wata alaka da asarar gashi ko kamanni.
Ya kara da cewa rashin haihuwa na iya zama daya daga cikin abubuwan da istimna’i ke haifar ga maza, yana mai cewa “yana iya haifar da matsalar rashin haihuwa”.
“Namijin da yake yin istimna’i kuma yana rasa maniyyi akai-akai yana iya samun raguwar adadin maniyyi yayin saduwa da mace.”
Hukunci
Da’awar cewa istimna’i yana daya daga cikin abubuwan farko dake haifar da asarar gashi a cikin maza, karya ne. A cewar kimiyya, al’aura da ja da baya na gashi ba su da wata alaƙa.