TheCable Fact Check
  • Home
  • Fact Check
  • Fake News
  • Check Am For Wazobia
Reading: Shin bidiyon rawa na Aregbesola yana da nasaba da soke takarar gwamna Oyetola?
Share
Latest News
Viral post wey claim sey dem don pass ‘Cybercrimes Act 2025’ no correct
Ózí na-ekwu nà é mepụ̀tálá ìwú megidere cybercrime bụ̀ àsị́
Irọ́ ni fídíò tó sọ pé Nàìjíríà ti sọ ‘Cybercrimes Act, 2025’ di òfin
Hoton hoto hoto ko bidiyo mai zagaya yanar gizo da sauri akan hanyar ”Dokar Laifukan gizo 2025′ karya ce
Fídíò Tinubu níbi tí ó ti ń rọ́ kẹ̀kẹ̀ mọ̀ àwọn ọmọ Nàìjíríà nítorí pé wọ́n pe ọ̀rọ̀ rẹ̀ ní AI kìí se òótọ́
Bidiyon Tinubu na barazana ga mutanen dake kirar maganar a matsayin AI, hadawa akayi
Video wey Tinubu dey threaten citizens wey call im statements AI na fake
Íhé ńgósị́ ébé Tinubu nà-àbárá ńdị́ ná-ákpọ́ ókwú ya AI bụ̀ ǹkè é nwòghàrị̀rị̀ énwòghárị́
Advertisement
Aa
TheCable Fact CheckTheCable Fact Check
Search
  • Home
  • Fact Check
  • Fake News
  • Check Am For Wazobia
Follow US

Shin bidiyon rawa na Aregbesola yana da nasaba da soke takarar gwamna Oyetola?

Ahmad Sahabi
By Ahmad Sahabi Published October 10, 2022 3 Min Read
Share

Wani faifan bidiyo da ke nuna Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan jihar Osun yana rawa a yanar gizo.

A shafin Twitter, an yada hoton bidiyon tare da ikirarin cewa ministan na rawa ne domin murnar soke zaben gwamnan Osun, Gboyega Oyetola a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar a jihar.

Wani mai shafi a Twitter, @IfedolapoOsun ne ya wallafa wannan sakon a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, a ranar da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke zaben Gboyega Oyetola da mataimakinsa, Benedict Alabi, a matsayin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC.

Aregbesola Today after Court Nullified Gboyega Oyetola's candidacy 🤣🤣 pic.twitter.com/2fEi8tbS1P

— Governor Ifedolapo Osun (@IfedolapoOsun) September 30, 2022

Bidiyon ya tattara kan 23,400 views, 879 likes da 352 retweets.

An raba bidiyon tare da taken “Aregbesola A Yau bayan Kotu ta soke takarar Gboyega Oyetola”.

Shafin Twittern da aka fara tura bidiyon na dauke ne da hoton Ademola Adeleke. Hakan ya ja hankalin wasu masu amfani da Twitter sukayi tunanin Ademola Adeleke, gwamna me jiran gado na Osun, ne ya tura bidiyon.

Abun da ya faru a baya

Alkalin kotun Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne a wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/468/2022 da jam’iyyar PDP ta shigar.

A karar, Mai Mala Buni, tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC, da wasu hudu sun kasance wadanda ake tuhuma.

Nwite, a hukuncin da ya yanke, ya ce nadin Oyetola da mataimakinsa ba bisa ka’ida ba ne, kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, domin Buni, wanda ya mika sunayensu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya saba tanadin sashe na 183 na kundin tsarin mulki da sashe na 82(3) ) na dokar zabe 2022.

Tabbatarwa

Binciken da TheCable ta yi ya nuna cewa wani ma’abocin Facebook, Ajiboye Maroof Akinlabi ne ya saka bidiyon a ranar Litinin, 26 ga Satumba, tare da bayanin: “Ministan harkokin cikin gida Ogbeni RAUF AREGBESOLA yana murnar cika shekaru 62 da haihuwar matarsa Ìyáàfin Sherifat Aregbesola”.

Kikiowo Ileowo, mataimaki na musamman ga Rauf Aregbesola, a lokacin da jaridar TheCable ta tuntubi ta, ya ce, “bikin ba shi da alaka da hukuncin da kotu ta yanke na soke Oyetola”, ya kara da cewa an dauki hoton bidiyon ne kwanaki da suka gabata a yayin bikin zagayowar ranar haihuwar matar Aregbesola.

Hukunci

Bidiyon raye-rayen da ake dangantawa da Aregbesola na murnar soke Oyetola na yaudara ne. An buga wani sigar farko a ranar Litinin, 23 ga Satumba, yayin da kotu ta yanke hukuncin a ranar Juma’a, 28 ga Satumba.

TAGGED: Aregbesola, Oyetola

Please send your feedback, claims to fact check and corrections requests to [email protected]

Ahmad Sahabi October 10, 2022 October 10, 2022
Share this Article
Facebook Twitter Email Copy Link Print
Leave a comment Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

POPULAR POSTS

Advertisement

Viral post wey claim sey dem don pass ‘Cybercrimes Act 2025’ no correct

One post for social media platforms claim sey di national assembly don pass di “Cybercrimes…

August 30, 2025

Ózí na-ekwu nà é mepụ̀tálá ìwú megidere cybercrime bụ̀ àsị́

Ózí a hụtara na soshal midia kwuru na ụlọ ọme iwu Naijiria emeputala iwu megidere…

August 30, 2025

Irọ́ ni fídíò tó sọ pé Nàìjíríà ti sọ ‘Cybercrimes Act, 2025’ di òfin

Ọ̀rọ̀ kan lori àwọn ohun ìgbàlódé íbaraẹnise orí ayélujára sọ pé ilé ìgbìmọ̀ asòfin àgbà…

August 30, 2025

Hoton hoto hoto ko bidiyo mai zagaya yanar gizo da sauri akan hanyar ”Dokar Laifukan gizo 2025′ karya ce

Wani rubutu da aka buga a dandalin sada zumunta ya yi iƙirarin cewa majalisar dokokin…

August 30, 2025
Advertisement
Advertisement

YOU MAY ALSO LIKE

Viral post wey claim sey dem don pass ‘Cybercrimes Act 2025’ no correct

One post for social media platforms claim sey di national assembly don pass di “Cybercrimes Act 2025” into law. Dem…

CHECK AM FOR WAZOBIA
August 30, 2025

Ózí na-ekwu nà é mepụ̀tálá ìwú megidere cybercrime bụ̀ àsị́

Ózí a hụtara na soshal midia kwuru na ụlọ ọme iwu Naijiria emeputala iwu megidere "mpụ e ji ịntanetị eme…

CHECK AM FOR WAZOBIA
August 30, 2025

Irọ́ ni fídíò tó sọ pé Nàìjíríà ti sọ ‘Cybercrimes Act, 2025’ di òfin

Ọ̀rọ̀ kan lori àwọn ohun ìgbàlódé íbaraẹnise orí ayélujára sọ pé ilé ìgbìmọ̀ asòfin àgbà ní orílẹ̀ èdè Nàìjíríà ti…

CHECK AM FOR WAZOBIA
August 30, 2025

Hoton hoto hoto ko bidiyo mai zagaya yanar gizo da sauri akan hanyar ”Dokar Laifukan gizo 2025′ karya ce

Wani rubutu da aka buga a dandalin sada zumunta ya yi iƙirarin cewa majalisar dokokin ƙasar ta amince da dokar…

CHECK AM FOR WAZOBIA
August 30, 2025

CableCheck seeks to provide reliable tools and resources for readers to tackle the menace of fake and misleading materials constantly pushed into the public space from various sources. We monitor the accuracy of claims made in traditional and social media. We also provide a tracker to hold politicians and policymakers accountable for the plans and promises they make to the public. CableCheck is a project of the Cable Newspaper Journalism Foundation (CNJF), supported by the MacArthur Foundation and implemented by TheCable newspaper.

Follow US: 

LINKS

  • Contact
  • About Us
  • Non-Partisanship Policy
  • Funding
  • Correction Policy
© Copyright TheCable. All Rights reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?