Shugaban kasar Kenya William Ruto a kwanakin baya yace shine shugaban kasa na farko daga nahiyar Afurka da a ka gayyata zuwa Amurka a cikin shekaru 20.
Ruto yayi wannan maganan ne a wani taro da Benny Hinn, wani fasto, ya shirya a Nairobi a Kenya, a ranar 24 da 25 na watan Febrairu.
“Shugaban kasar Amurka ya gayyaci shugaban kasar Kenya zuwa Amurka. Ba a taba yin hakan ba a shekaru 20 da suka wuce, babu wani shugaban kasa da aka gayyata zuwa Amurka,” Ruto ya sanar.
Bidiyon sa ya na magana, wanda Citizen TV ta haska, mutane sama da mutane 239,000 sun kalla a cikin kwana 11 a shafin su na Youtube inda ke da mabiya sama da mutane miliyan hudu.
Maganan da Ruto yayi ya bull a kafar sada zumunta na X( wanda aka fi sani da Twitter a da), inda wadansu suka daura maganan Ruto, wasu kuma suna murnar maganan da yayi.
Yayin da wani mai shafi a X mai suna Sirengo Maurice yace Ruto “zai haska Kenya a idon duniya a wanna tafiyan da zai shiga tarihi”, wani mai shafin daban ya ce meye amfanin maganan da shugaban yayi a taro na addini.
MENENE ZIYARAR DA AKE KIRA STATE VISIT WANDA RUTO ZAI YI ZUWA AMURKA?
Ziyarar state visit, ziyara ne wanda shugaban wata kasa keyi zuwa kasa yawanci a bisa gayyata.
Osita Agbu, wani farfesa a jami’ar Baze a Abujan Najeriya, yace wasu ziyaran nada “matukar amfani” da kuma “fa’ida”, saboda yana ba shuagabanni daman su tattauna abubuwa masu amfani.
A Amurka, ana daukan ziyarar state visit a matsayin babban karramawa da kuma alaman son karfafa alaka tsakanin kasar da aka gayyata shugaban ta sannan ziyarar yawanci baya wuce tsawon kwana hudu a tare da wasu taro da za a shirya.
Sun hada da cin abinci a fadar shugaban kasar Amurka wato White House, luncheon, da kuma bama shugaban da aka gayyata Blair House a matsayin masaukin sa.
Blair House ne inda ake sauke manyan bakin da aka gayyata ko suka kai ziyara Washington DC. Ana kuma kiran Blair House din masaukin bakin shugaban kasa.
Yawani ziyarar state visit don ayi murnar karfafa alaka ne tsakanin kasashe ake yin sa.
TABBATAR DA MAGANAR RUTO
Don tabbatar da maganar da Ruto yayi, TheCable ta binciko shuagabannin da suka kai ziyara zuwa Amurka a shekarun baya.
Shugaba Edwin Barclay na Laberiya ne na farko daga Afurka da ya fara kai ziyara Amurka a 1943 a lokacin mulkin Franklin Roosevelt, shugaban kasar Amurka na 32.
A 2008 – shekaru 16 da suka wuce – John Kuffour, tsohon shugaban kasar Ghana, tare da matar sa sunkai ziyara Amurka inda George Bush, shugana Amurka na 43, ya tarbe su.
Bush ya nuna farin cikin sa da Kuffor tare da mukarraban sa suka amsa gayyatan shi.
Kafun Kuffor ya kai ziyarar shi a 2008, Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya na uku, shima ya kai ziyara zuwa Amurka a lokacin Bush a Oktoban 2003.
HUKUNCI
Maganar da shugaba Ruto yayi ba dai-dai bane. Duk da dai shine shugaban kasar Kenya na farko da ya kai ziyara zuwa Amurka a sama da shekaru 20, ba shi bane na farko a Afurka gaba daya ba da aka aikama gayyatan zuwa state visit a Amurka ba a shekaru 20.