TheCable Fact Check
  • Home
  • Fact Check
  • Fake News
  • Check Am For Wazobia
Reading: BINCIKEN GASKIYA: A’a, bidiyon da ke yawo bana daukan fansan sojoji bane a kan kisan Okuama
Share
Latest News
FACT CHECK: Is Nigeria 4th fastest-growing economy in the world in 2025?
FACT CHECK: How true are Obi’s claims about poverty rate in Nigeria, China and Indonesia?
FACT CHECK: No, Finnish court didn’t approve Simon Ekpa’s extradition to Nigeria
FACT CHECK: Is Cardinal Arinze eligible to be elected as the next Pope?
Rárá, Jonathan kò sọ pé Tinubu yóò se àṣeyọrí nínú ètò ìdìbò fún Ipò Ààrẹ ní ọdún 2027
A’a, Jonathan bai yi hasashen nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027 ba
No, Jonathan no predict Tinubu victory for 2027 presidential election
Ḿbà, Jonathan ágbaghị àmà na Tinubu gà-èmérí ńtùlíáka ónyé ísíàlà ǹkè áfọ̀ 2027
Advertisement
Aa
TheCable Fact CheckTheCable Fact Check
Search
  • Home
  • Fact Check
  • Fake News
  • Check Am For Wazobia
Follow US

BINCIKEN GASKIYA: A’a, bidiyon da ke yawo bana daukan fansan sojoji bane a kan kisan Okuama

Ahmad Sahabi
By Ahmad Sahabi Published March 31, 2024 2 Min Read
Share
Screenshot

Wani labari a shafukan sada zumunta na cewa sojin Najeriya sun dauka fansa a garin Okuama, a jihar Delta biyo bayan kashe sojoji 17 da akayi.

Ana ta yada wani bidiyo a matsayin shaida cewa sojoji suna daukan fansa.

A ranar 14 ga watan Maris  wasu matasa suka kashe sojoji 17 a garin Okuama.

Mutuwar sojojin ya tayar da kura a fadin kasar – sannan ana ta zargin cewa sojoji sun dauka fansa ta kona gaba daya garin.

“Okuama a garin Delta na ci da wuta da safen nan. Sojoji sun dauka kaddamar da yaki a yankin,” inji @EmekaGift100, wani mai shafi a X da ya dauran bidiyon.

Ya kuma ce shi mai kare hakkin danAdam ne kuma mai kare masu neman kafa kasar Biafra.

Mutune sama da 97,200 sun ga abubuwan da ya daura a shafin sa, 706 sun sake turawa, 581 sun danna alaman so, sannan 181 sunyi sharhi a kai.

A bidiyon mai tsawon dakika 54, a na iya ganin kwale kwale na ci da wuta kuma hayaki na tashi.

“Hakan ya dache?” Inji wani yayin da wutan ke kara ci.

A cewar @EmekaGift100, sojoji sun tayar da wutan ne don su “kona kananan yara da mata” da ran su.

Somto Okonokwo, wani mai shafi a X, shima yayi magana mai shigen na farkon da a ka yi, ya kara da cewa sojoji na kai ma mutane masu zama a kudu hari sannan suna kare masu zama a arewa.

TABBATARWA

TheCable ta yi bincike a kan bidiyon inda ta gano cewa an taba daura bidiyon a TikTok a karshe-karshen watan Janairu – kusan wata biyu kenan kafun kisan sojojin da a ka yi a Delta.

Sanda aka fara daura bidiyon, an alakanta shi ne ga wani gobara da aka a jihar Ribas.

Bincike ya nuna an buga labaran gobarar a watan Janairun 2024 wanda ya yi sanadiya asarar dukiya a jihar Ribas.

HUKUNCI

Bidiyon ba ya nuna cewa a garin Okuama na jihar Delta ne ya kama da wuta.

TAGGED: Okuama community, soldiers killings

Please send your feedback, claims to fact check and corrections requests to [email protected]

Ahmad Sahabi April 8, 2024 March 31, 2024
Share this Article
Facebook Twitter Email Copy Link Print
Leave a comment Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

POPULAR POSTS

Advertisement

FACT CHECK: Is Nigeria 4th fastest-growing economy in the world in 2025?

A viral post claims, based on International Monetary Fund (IMF) projections, that Nigeria ranks fourth…

May 9, 2025

FACT CHECK: How true are Obi’s claims about poverty rate in Nigeria, China and Indonesia?

Peter Obi, Labour Party (LP) presidential candidate in the 2023 elections, sparked a debate with…

May 5, 2025

FACT CHECK: No, Finnish court didn’t approve Simon Ekpa’s extradition to Nigeria

On Tuesday, some social media users and blog sites made a post claiming that a…

April 24, 2025

FACT CHECK: Is Cardinal Arinze eligible to be elected as the next Pope?

A social media user has claimed that Francis Arinze, a Roman Catholic cardinal, is the…

April 21, 2025
Advertisement
Advertisement

YOU MAY ALSO LIKE

Rárá, Jonathan kò sọ pé Tinubu yóò se àṣeyọrí nínú ètò ìdìbò fún Ipò Ààrẹ ní ọdún 2027

Ní ọjọ́ ajé, ọ̀rọ̀ kan to sọ pé Goodluck Jonathan, Ààrẹ orílẹ̀ èdè Nàìjíríà tẹ́lẹ̀ sọ pé Ààrẹ Bọla Tinubu…

CHECK AM FOR WAZOBIA
April 20, 2025

A’a, Jonathan bai yi hasashen nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027 ba

A ranar Talata ne wani rahoto da ke ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi hasashen nasarar Shugaba…

CHECK AM FOR WAZOBIA
April 20, 2025

No, Jonathan no predict Tinubu victory for 2027 presidential election

On Tuesday, one report wey claim sey former President Goodluck Jonathan predict President Bola Tinubu victory for di 2027 presidential…

CHECK AM FOR WAZOBIA
April 20, 2025

Ḿbà, Jonathan ágbaghị àmà na Tinubu gà-èmérí ńtùlíáka ónyé ísíàlà ǹkè áfọ̀ 2027

N’ubọchị Tuesde, ozi na-ekwu na onye bụburu onye isiala Naijiria, bụ Goodluck Jonathan, gbara àmà na onyeisiala Bola Tinubu ga-emeri…

CHECK AM FOR WAZOBIA
April 19, 2025

CableCheck seeks to provide reliable tools and resources for readers to tackle the menace of fake and misleading materials constantly pushed into the public space from various sources. We monitor the accuracy of claims made in traditional and social media. We also provide a tracker to hold politicians and policymakers accountable for the plans and promises they make to the public. CableCheck is a project of the Cable Newspaper Journalism Foundation (CNJF), supported by the MacArthur Foundation and implemented by TheCable newspaper.

Follow US: 

LINKS

  • Contact
  • About Us
  • Non-Partisanship Policy
  • Funding
  • Correction Policy
© Copyright TheCable. All Rights reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?