Jam’iyar United Party for National Development (UNDP) tayi watsi da wani bidiyo dake yawo dake nuna shugaba Hakainde Hichilema na Zambiya ya na cewa ba zai sake tsaya wa takara ba a zaben 2026.
A bidyon da ke ta yawo, ana iya ganin Hichilema sanye da kwat tare da tutar kasar Zambiya a bayan sa, ya na bayyana cewa ba zai nema yin tazarce ba a zaben da za a gudanar da kasar a 2026.
“Ina so shaida cewa ina sane da kalubalen da aka fuskanta a karkashin mulki na a matsayi na na shugaban wannan kasa mai albarka. Ina so na sanar da cewa ba zan yi takara ba a zaben da za ayi a 2026. A tunani na, wannan hukuncin dana dauka shine yafi don ci gaban kasar mu,” inji shi.
Hichilema yayi takaran shugaban kasa so biyar bai ci ba kafun yayi nasara daga baya a 2021.
A Zambiya, ana zaben shugaban kasa yayi shekaru 5 yana mulki kuma wa’adi biyu.
Idan aka ma bidiyo kallo na kusa-kusa, za aga motsin bakin da fitar maganar sa ba a tare suke tafiya ba, sannan bayan bidiyon yayi dishi-dishi. Ta nan za a gane anyi amfani da artificial intelligence (AI) a hada bidiyon.
Bidiyon na zuwa ne a lokacin da siyasar kasar Zambiya ke daukan zafi kafun zaben da za ayi a kasar a 2026.
Kamar yadda ake yi a sauran kasashe, idan lokacin zabe ya gabato, ana yawan yada bidiyoyi na karya don a yaudari mutane ko chanza musu tunani akan wadansu ‘yan takara.
A wata sanarwa da Batuke Imenda, sakatare janar na jam’iyar UPND mai mulki a Zambiya, ya zargi “yan bata gari” da “hadawa tare da yada bidiyoyi na karya da akayi amfani da muryar shugaban kasar da manufar a yaudari jama’a”.
“Mun fahimci wannan aiki ne na ‘yan adawa. Gaggawarsu har ya kai ga sun fara niyyan aikata laifi a kan shugaban da ‘yan kasa suka zaba,” inji sanarwar.
“Mun san wasu shuagabannin ‘yan adawa suna nan suna ta kokarin yin abubuwa da zasu janyo ma gwamnati mai mulki tarzoma.
“Mun san kuna neman mabiya ne kuma ku samu karbuwa amma zamu tunatar daku cewa doka makaho ne.
“Ba boyeyyen abu bane cewa wasu daga cikin ku suna abubuwan da suka sabawa doka don janyo hankalin jami’an tsaro. Sannan da zarar an kama ku don yin bincike, kune kuka fi kowa ihu.
“Jam’iyar tana so tayi kira ga duk wanda keda hannu a wannan bidiyon da ke ta yawo cewa zai kwashi kashin shi a hannu idan hukuma ta kama shi.”
Shugaban kasar bai ce komai ba har yanzu a game da bidiyon.
Saidai, rundunar ‘yan sandan kasar sunce sun fara bincike don gano wadanda suka hada bidiyon don a kama su kuma a hukuntasu.