Bello el-Rufai, mai wakiltar Kaduna ta arewa a majalisar tarayya, yace Hadiza Balarabe ce mace ta farko da aka zaba a matsayin mataimakiyar gwamna a Najeriya.
Danmajalisan yayi maganan ne a wani shiri da yayi da Seun Okinbaloye, wani babban dan jarida.
Shirin nada mabiya 16,300, mutane 94,760 sun gani, 602 sunyi sharhi a kai sannan 2,900 sun danna alaman so a kai.
Bello da ne ga Nasir el-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna.
A 2018, Nasir el-Rufai ya dauka Balarabe a matsayin mataimakiyar sa a zaben gwamnan 2019.
Yace ya dauka Balarabe ne saboda Barnabas Bantex, matainakinsa na lokacin, ya sanar da shi cewa zai yi takaran zama sanata.
Kafun ta zama mataimakiyar el-Rufai, Balarabe be shugaban cibiyoyin kiwon lafia na Kaduna.
TABBATARWA
Da yake magana a kan ayyukan da baban shi yayi a Kaduna, danmajalisan yace baban shi, ta Balarabe ya gyara duka cibiyoyin kiwon lafia 255 da ke jihar.
“Daya daga cikin abubuwan da babana yayi tare da mataimakiyar sa, Dr. Hadiza (Balarabe), wanda itace mataimakiyar gwamna mace ta farko da aka zaba a Najeriya shine gyara duka cibiyoyin kiwon lafia 255 dake Kaduna,” inji dan majalisar.
Saidai, bincike da TheCable tayi ya nuna tun da a ka dawo dimokradiya a 1999, Najeriya ta samu mataimakan gwamna mata banda Balarabe.
MATA DA SUKA YI MATAIMAKAN GWAMNA
Jihar Legas ne na farko a zaben mace a matsayin mataimakiyar gwamna. A 1992, a lokacin da a aka yi mulkin dimokradiya na wani dan kankanin lokaci, Micheal Otedola ya zama gwamnan Legas a karkashin National Republic Convention (NRC) tare da Sinatu Ojikutu a mataimakiyar sa.
Ojikutu yayi gwamna har zuwa Nuwamban 1993 da aka yi juyin mulki.
A 1999, Najeriya ta koma mulkin dimokradiya. Bola Tinubu ya lashe zaben gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyar Alliance for Democracy (AD) tare da Kofoworola Akerele-Bucknor a mataimakiyar sa.
Tun daga lokacin, irin su Adebisi Sosan, Adejoke Orelope-Adefurile, da Oluranti Adebule duk sun yi mataimakan gwanma a Legas tsakanin 2007 da 2019.
Abiodun Olumiji tayi ma Ayo Fayose mataimakiyar gwamna daga Satumban 2005 zuwa 2006. Funmilayo Olayinka tayi ma Kayode Fayemi mataimakiya daga 2010 zuwa 2013 inda ta mutu sannan Modube Adelabu ta zama mataimakiyar gwamna a 2013.
A jihar Ogun, Salimat Badru tayi mataimakiyar gwamna daga 2003 zuwa 2011, sannan Yetunde Onanuga tayi mataimakiyar gwamna a jihar daga 2015 zuwa 2019.
A Osun, Olusa Obada tayi mataimakiyar gwamna daga 2003 zuwa 2010 lokacin mulkin Olagunsoye Oyinlola, sannan Titilayi Laoye-Tomori ta zama mataimakiyar gwamnan jihar daga 2010 zuwa 2018.
Pauline Tallen ta zama mataimakiyar gwamna a jihar Filato a 2007, inda ta zama mataimakiyar gwamna mace ta farko a arewacin Najeriya sannan Ipalibo Banigo tayi ma Nyesom Wike mataimakiya a jihar Ribas daga 2015 zuwa 2023.
Cecilia Ezeilo tayi ma Ifeanyi Ugwuanyi mataimakiyar gwamna bayan yaci zabe a 2015.
Noimot Salako-Oyedele ta zama mataimakiyar Dapo Abiodun a jihar Ogun a 2019, shekarar da aka rantsar da Balarabe a matsayin mataimakiyar gwamnan Kaduna.
A 2022, an zaba Balarabe a matsayin mataimakiyar Uba Sani. A Maris na 2023, an sake zaben ta a matsayin mataimakiyar gwamna.
HUKUNCI
Maganar da Bello el-Rufai yayi cewa Balarabe mataimakiyar gwamna mace ta farko da a ka zaba a Najeriya ba dai-dai bane.
Sinatu Ojikutu ce mataimakiyar gwamna mace ta farko da a ka zaba.