Wani labari a shafukan sada zumunta na cewa sojin Najeriya sun dauka fansa a garin Okuama, a jihar Delta biyo bayan kashe sojoji 17 da akayi.
Ana ta yada wani bidiyo a matsayin shaida cewa sojoji suna daukan fansa.
A ranar 14 ga watan Maris wasu matasa suka kashe sojoji 17 a garin Okuama.
Mutuwar sojojin ya tayar da kura a fadin kasar – sannan ana ta zargin cewa sojoji sun dauka fansa ta kona gaba daya garin.
“Okuama a garin Delta na ci da wuta da safen nan. Sojoji sun dauka kaddamar da yaki a yankin,” inji @EmekaGift100, wani mai shafi a X da ya dauran bidiyon.
Ya kuma ce shi mai kare hakkin danAdam ne kuma mai kare masu neman kafa kasar Biafra.
Mutune sama da 97,200 sun ga abubuwan da ya daura a shafin sa, 706 sun sake turawa, 581 sun danna alaman so, sannan 181 sunyi sharhi a kai.
A bidiyon mai tsawon dakika 54, a na iya ganin kwale kwale na ci da wuta kuma hayaki na tashi.
“Hakan ya dache?” Inji wani yayin da wutan ke kara ci.
A cewar @EmekaGift100, sojoji sun tayar da wutan ne don su “kona kananan yara da mata” da ran su.
Somto Okonokwo, wani mai shafi a X, shima yayi magana mai shigen na farkon da a ka yi, ya kara da cewa sojoji na kai ma mutane masu zama a kudu hari sannan suna kare masu zama a arewa.
TABBATARWA
TheCable ta yi bincike a kan bidiyon inda ta gano cewa an taba daura bidiyon a TikTok a karshe-karshen watan Janairu – kusan wata biyu kenan kafun kisan sojojin da a ka yi a Delta.
Sanda aka fara daura bidiyon, an alakanta shi ne ga wani gobara da aka a jihar Ribas.
Bincike ya nuna an buga labaran gobarar a watan Janairun 2024 wanda ya yi sanadiya asarar dukiya a jihar Ribas.
HUKUNCI
Bidiyon ba ya nuna cewa a garin Okuama na jihar Delta ne ya kama da wuta.