Wani faifan bidiyo da ke nuna Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan jihar Osun yana rawa a yanar gizo.
A shafin Twitter, an yada hoton bidiyon tare da ikirarin cewa ministan na rawa ne domin murnar soke zaben gwamnan Osun, Gboyega Oyetola a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar a jihar.
Wani mai shafi a Twitter, @IfedolapoOsun ne ya wallafa wannan sakon a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, a ranar da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke zaben Gboyega Oyetola da mataimakinsa, Benedict Alabi, a matsayin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC.
Aregbesola Today after Court Nullified Gboyega Oyetola's candidacy 🤣🤣 pic.twitter.com/2fEi8tbS1P
— Governor Ifedolapo Osun (@IfedolapoOsun) September 30, 2022
Bidiyon ya tattara kan 23,400 views, 879 likes da 352 retweets.
An raba bidiyon tare da taken “Aregbesola A Yau bayan Kotu ta soke takarar Gboyega Oyetola”.
Shafin Twittern da aka fara tura bidiyon na dauke ne da hoton Ademola Adeleke. Hakan ya ja hankalin wasu masu amfani da Twitter sukayi tunanin Ademola Adeleke, gwamna me jiran gado na Osun, ne ya tura bidiyon.
Abun da ya faru a baya
Alkalin kotun Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne a wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/468/2022 da jam’iyyar PDP ta shigar.
A karar, Mai Mala Buni, tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC, da wasu hudu sun kasance wadanda ake tuhuma.
Nwite, a hukuncin da ya yanke, ya ce nadin Oyetola da mataimakinsa ba bisa ka’ida ba ne, kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, domin Buni, wanda ya mika sunayensu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya saba tanadin sashe na 183 na kundin tsarin mulki da sashe na 82(3) ) na dokar zabe 2022.
Tabbatarwa
Binciken da TheCable ta yi ya nuna cewa wani ma’abocin Facebook, Ajiboye Maroof Akinlabi ne ya saka bidiyon a ranar Litinin, 26 ga Satumba, tare da bayanin: “Ministan harkokin cikin gida Ogbeni RAUF AREGBESOLA yana murnar cika shekaru 62 da haihuwar matarsa Ìyáàfin Sherifat Aregbesola”.
Kikiowo Ileowo, mataimaki na musamman ga Rauf Aregbesola, a lokacin da jaridar TheCable ta tuntubi ta, ya ce, “bikin ba shi da alaka da hukuncin da kotu ta yanke na soke Oyetola”, ya kara da cewa an dauki hoton bidiyon ne kwanaki da suka gabata a yayin bikin zagayowar ranar haihuwar matar Aregbesola.
Hukunci
Bidiyon raye-rayen da ake dangantawa da Aregbesola na murnar soke Oyetola na yaudara ne. An buga wani sigar farko a ranar Litinin, 23 ga Satumba, yayin da kotu ta yanke hukuncin a ranar Juma’a, 28 ga Satumba.