Wani bidiyon Abdulrahman Abdulrazaq, gwamnan jihar Kwara, dandazon jama’a nayi masa ihu ya bulla a yanar gizo.
A cikin dandazon jama’a ana jin mutane na kiran gwamnan ‘Ole’ da yaren yarbanci wanda ke nufin barawo yayin da ake masa ihu da zai bar wurin wani taro.
Wadanda suka yada bidiyon sunce abun ya faru ne kwanan nan sanda gwamnan da wasu ‘yan jam’iyar All progressives Congress (APC) suka ziyarci polytechnic din jihar Kwara domin gudanar da taro na siyasa.
An tura bidiyon a wani shafin Facebook, Peter Obi Support Group, a rananr Litinin inda sama da mutane 2,600 suka kalla.
Wani shafi mai suna Nigeria Youth Movement shima ya tura bidiyon tare da rubutun:”Mutanen da suka bar APC zuwa PDP na koran gwamnan jihar Kwara, suna ihun sai Buky Bukola Saraki”. Mutane sama da 1,200 sun kalla bidiyon da aka tura shi ranan Talata.
Banda Facebook, an tura bidiyon zuwa Youtube, Whatsapp da TikTok.
Wani shafin Youtube, E-vibez TV, daya tura bidiyon ranan Litinin, yace Abdulrazaq na kokarin yin camfen na karin zaben sa a shekarar 2023. A shafin, sama da mutane 7,900 suka kalli bidiyon.
Tabbatarwa
TheCable ta saka bidiyon a InVID, na’uran gudanar da bincike a yanar gizo inda yanuna cewa farko bidiyon an tura shi a Youtube a shekarar 2018.
Bidiyon an fara tura shi ne a Youtube a shafin, Kwara Fist, a ranar 25 ga watan Disamba 2018, tare da rubutun: “An samu barkewan rikici a Ilorin a wurin taro na 53 na shekara shekara na Ilorin Emirate Progressive Descendent Union (IEPDU) sanda magoya bayan shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki suka kwace ragamar gudanar da taron”.
A ranar 9 ga watan Agusta, gwamnatin jihar Kwara tayi magana a game da bidiyon a wata sanarwa data daura a shafin ta na Facebook.
Sanarwan da Bashir Adigun, mataimakin gwamnan akan hulda da jama’a akan harkan siyasa, da aka yi wa taken: “Bidiyon karya akan gwamna AbdulRazaq: Tunatarwa akan rashin ci gaban Kwara”.
Adigun yace Bidiyon an dauke shi ne a ranar 26 ga watan Disamban 2018, sanda ‘yan daba da kuma magoya bayan Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattijai, ya yi gargadi a taron da Ilorin Emirate Descendents Progressive Union (IEDPU).
Adigun ya ce bidiyon an dauke shi ne sanda gwamnan yana dan takaran gwamna a jihar inda ya halarci taro a matsayin babban bako a garin da ya fito.
Ya kara da cewa babu wani taro daya gudana a makarantan Polytechnic na Kwara a ranar 7 ga watan Agusta, da zai iya nuna cewa gwamnan ya harci taron.
“Wadanda suka turo bidiyon sunyi shi ne da niyyan a ce ana yi wa gwamna mai mulki ihu,” inji shi.
Hukunci
Bidiyon dake nuna dandazon jama’a nayi wa gwamnan jihar Kwara ihu na yaudara ne. Tsohon bidiyo ne da aka dauke shi tun shekarar 2018. Ba sabon bidiyo bane da aka dauka kwanan nan.