Wani bidiyo dake nuna Ayuba Elkana, kwamishinan yan sanda na jihar Zamfara, yana shaida cewar sun samu wata wasikar barazana daga wurin yan ta’adda dake umurtar mabiya addinin Kirista dake jihar Zamfara dasu rufe duka cocunan dake jihar na tsawon wata uku na ta yaďuwa a shafukan sada zumunta.
An tura bidiyon a shafin Facebook, Twitter da Whatsapp.
“Yan sanda sun tabbatar da sun samu wasikar barazana dake umurtan mabiya addinin Kirista dasu rufe cocunan dake Nijeriya na tsawon wata uku”, rubutun da wani yayi a karkashin bidiyon kenan a shafin sa na Facebook a ranar 14 ga watan Yuni.
Shafin Facebook din yana da Mabiya sama da dubu dari da sha biyu (112,000). Mutane sama da dubu dari da sittin da biyar (165,000) sun kalla bidiyon, da kuma mutane sama da dari bakwai da hamsin (750) sun yi sharhi akai sannan mutane sama da dubu takwas da dari biyu (8,200) sun tura bidiyon.
Sharhin da akayi a karkashin bidiyon dakuma labarin dayake dauke da, ya nuna cewa mutane da yawa sun gamsu da abin da suka gani.
TABBATARWA
Wani bincike da TheCable ya yi ya nuna cewa bidiyon da ke yawo ya tsufa kuma an yi shi a cikin 2021.
Anyi bidiyon a jihar Zamfara, inda Elkana ya gana da manema labarai a ranar 30 ga watan Nuwamban 2021. Yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Gusau, babban birnin jihar, Elkana ya shaida wa manema labarai cewa yan sanda sun samu wasikar barazana daga yan ta’adda dake umurtan mabiya addinin Kirista dasu rufe cocunan dake jihar na tsawon shekara uku, ko kuma sun fuskanci barazanar harin da ze biyo baya.
“An ajiye wasikar ne a kofar shiga ofishin yan sandan jihar” inji kwamishinan yan sandan jihar.
Yayin da yake magana akan shirye-shiryen da jami’an tsaro keyi akan matsalar tsaro, kwamishinan yace wasikar na dauke da sunayen wasu cocuna dake waje-wajen babban birnin jihar da za a kai wa hare-hare lokacin da ake cikin bauta kafun karshen shekarar 2021.
Jaridar TheCable ta tuntubi Iliya Tsiga, shugaban kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar Zamfara, yace bidiyon dake yawo tsohon bidiyo ne.
“Naga bidiyon dakuke magana. Tsohon bidiyo ne tun watan Nuwamban 2021. Ana sake yaďa shi ne. Wannan batun an riga da an shawo kanshi; kuma wanda ya tura wannan bidiyon kawai yana neman tayar da zaune tsaye ne,” inji Tsiga.
“Wasikar an yi shi ne a matsayin barazana ga duka mabiya addinin Kirista dake jihar. Basu bayyana wata kabila ba. Muna kira ga jama’a dasu yi watsi da bidiyon da hoton kuma su ci gaba da harkoki da alamuran rayuwa na yau da kullun”.
HUKUNCI
Bidiyon dake yawo tsohon bidiyo ne tun shekarar 2021, labarin da yake dauke da shi da ke cewa yan ta’adda sun umarci a rufe cocuna a fadin kasar nan na tsawon wata uku ba gaskiya bane.